Kotun ɗaukaka ƙara ta mayar wa Gwamna Sule na Nasarawa nasararsa ABDULLAHI SULE
- Mufkufam
- Nov 23, 2023
- 1 min read
Gwamnan jihar Nasarawa
Kotun ɗaukaka ƙara da ke zaman ta a Abuja ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron ƙorafin zaɓen jihar Nasarawa, inda ta mayar wa Gwamna Abdullahi Sule nasara kamar yadda hukumar INEC ta bayyana a lokacin zaɓen gwamnan jihar na 2023.
A hukuncin da kotun ta yanke yau Alhamis, alƙalan kotun sun bayyana cewa kotun sauraron ƙorafin zaɓen gwamnan jihar Nasarawa ta yi kuskure a hukuncin da ta yanke.
A watan da ya gabata ne dai kotun sauraron ƙorafin zaɓen jihar Nassarawa ta soke nasarar gwamna Abdullahi Sule na jam'iyyar APC, tare da bayyana David Ombugadu na PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen na watan Maris ɗin 2023.
Comments